Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya (SGF) a matsayin ma'aikacin gwamnati mai kwazon gaske.

Yana mai cewa yaki da cutar Covid-19 na kasa na karkashinsa, don haka ya cancanci yabo na musamman.

Boss Mustapha
Boss Mustapha

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ta taya Mustapha murnar cika shekaru 65 a duniya, kamar yadda Radio Nigeria Kaduna ta ruwaito.

Shugaban ya bayyana cewa "tun lokacin da aka nada Mustapha matsayin sakataren gwamnatin tarayya, girmamawa da kuma son da ya ke wa Mustapha suka karu sosai cikin zuciyarsa, saboda yadda ya ke aikinsa cikin karsashi da kuzari."

Yace "Mr.  Mustapha mutumin kirki ne mai son kwarin-guiwa da goyon bayan abokan aikinsa."

Buhari ya kara yaba wa Boss Mustapha saboda "ya taka rawa sosai da ba ta misaltuwa a kasar wajen yaki da cutar Covid-19".

Shugaba Buhari ya yi kira ga "sauran ma'aikatan gwamnati da su yi koyi da Boss Mustapha wanda yana yin aikinsa ne cikin karsashi da ban mamaki."

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba