Fitaccen jarumin masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood, Sulaiman Bosho, ya kai ziyara ta musamman sabon gidan talibijin din Sunnah TV.

Manajan Darakta (MD) na gidan talibijin din, Dr Ibrahin Isah Disina, shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya yi a kafar sada zumunta ta Facebook.

Dr Isa Disina da Sulaiman Bosho
Dr Isa Disina da Sulaiman Bosho

Kazalika jarumin, ya bayar da gudunmawa irin tasa, domin karawa aikin gina sabon ofishin Sunna Tv karsashi.

Malamin ya bayyana mamakinsa, duba da yadda Bosho ke al'amuransa na matsayin jarumi, amma duk da haka har ya samu damar yin irin wannan gwaggwaban aiki.

Haka kuma abin ya matukar baiwa MD na Sunna TB sha'awa, yadda jarumin ya subar da hawaye, kana Dr Disina ya yiwa jarumin addu'a da fatan alkhairi.

Dr. Isa Disina, ya bayyana haka ne a shafinsa na sada zumunta na facebook, inda ya wallafa:

"BOSHO A SUNNAH TV"

"Ya kawo mana ziyarar bazata a sabon ofishin Sunna TV da ake kan aikinsa ya bada gudunmawa irin tasa!!."

"Abin ya bani sha'awa, yadda ya zubar da hawaye!!."

"Allah ka habaka masa imaninsa, ya karbi kyawawan aikyukanmu ya gafarta mana kurakurenmu."

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba