Yan bindiga sun sake sace yara a wata makaranta a mahaifar Gwamnan Zamfara

Yau laraba wasu 'yan bindiga sun sace daliban makarantar boko a Zamfara.

Har yanzu ba'a tabbatar da adadin yawan daliban da 'yan bindigar suka yi awon gaba da su ba, amma dai sun sace su ne a makarantar Kaya, da ke Karamar Hukumar Maradun.

Gwamna Matawalle
Gov Matawalle, Zamfara State

Garin Kaya shine mahaifar Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle.

Kamar yadda wani mazaunin garin Kaya ya shauda wa jaridar PremiumTimes yace, daliban an sace su ne a makaranta ranar laraba.

"Kana yace bai san iya adadin daliban da 'yan bindigar suka yi awon gaba da su ba, amma dai dalibai da malamai da dama sun tsere gida."

Zuwa yanzu labari ya isa zuwa ga Gwamnan Zamfara, yanzu haka kuma yana cikin ganawar tsaro kan wannan sabuwar satar daliban.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba