Auta kuma ta ƙarshe cikin ƴaƴan Shugaban Buhari, wato Noor Buhari ta fito gaba-gaɗi ta bayyanawa tsohonta burinta na auren ɗan talaka.

Wannan jawabi ya fito ne a cikin wata magana da autar uwargidan shugaban ƙasar ta wallafa a kafar sada zumunta ta Instagram.

Noor Buhari
Noor Muhammadu Buhari

Inda ta fito tsakaninta da Allah ta bayyana muradinta na auren talaka, domin nuna halacci ga sauran talakawan Najeriya ga irin soyayyarsu ga babanta Buhari. Kamar yadda shafin HausaLoaded ya ruwaito.

Ni dan talakka zan aura domin nuna halacci ga talakkawan Najeriya da suka nuna soyayyar su ga Babana. Inji Noor Buhari.

Wannan amsa ta ɗiya kuma ƴar autar Buhari, Noor ta biyo-bayan yawan tambayoyi da ƴan Najeriya ke damunta da su, 'Shin ko talaka za ta aura?'.

Noor, asalin sunansa shine, Amina Muhammadu Buhari, kuma ta kasance ƴar auta cikin ƴaƴan shugaban Najeriya, Buhari.

Idan baku manta ba, Buhari ya aurar da dukkanin ƴaƴansa mata da maza, tun daga kan su Zahra har zuwa Yusuf, yanzu sauran Noor kaɗai.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba