Nagartacciyar majiya ta tabbatar da mutuwar wasu mutum biyu mazauna kauyen Makoro Iri da ke Karamar Hukumar Kujuru ta jihar Kaduna

Nasir El-rufa'i
Nasir El-rufai, Gwamnan Kaduna

Mutuwar ta su ta biyo-bayan dirar mikiyar da 'yan bindiga su ka yi a kauyen na Makoro Iri, tare da mamaye shi.

Inda suka binduge wani wanda ake kira da Gideon Mumini da Barnabaz Ezra har lahira, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wannan rahoto dai Kwamishinan Tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana shi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi 29 ga watan Agustan 2021.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba