Fitaccen malamin addinin nan mabiyin darikar Tijjaniyya, Farfesa Ibrahim Makari ya ce ya janye karar da ya shigan akan Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya.

Makari da Gadon Kaya
image source: Freedom Radio

Malamin ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da Freedom Radio, yace ya janye karar ne sakamakon magabatansa da suka shiga maganar, ciki har da mahaifinsa.

Sai dai malamin ya ce, duk da haka, ya barwa Allah al'amarin ya musu hukunci ranar sakamako.

Ya ce lauyoyinsa yanzu haka na kokarin janye karar, domin an shigar da ita karar kotunan musulunci biyu.

A karse Farfesa Maqari ya yi kira ga dalibansa da ransu ya matukar sosu da su yi hakuri bisa wannan mataki da ya dauka.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba