Rundunar 'yan sandan Najeriya, reshen jihar Nasawa ta cafke wani matashi kan basajar saka kakin sojojin ruwa da damfarar mutane yayin da ta kai wani sumame.

'Yan Sandan Najeriya
'Yan sandan Najeriya

Matashin mai shekara 32, mai suna Nasiru Ahmad, an kama shi ne a karamar hukumar Karu, kusa da babban birnin jihar kan basajar saka kakin sojojin ruwa, da nuna eh shi din ma sojan ruwa ne.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jigar, ASP Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa cewa sun kama jami'in sojan ruwa na karya ne yayin wani samame da jami'an 'yan sanda suka kai a karamar hukumar Karu.

A cewar sanarwar, Nasiru Ahmed wanda ya yi shigar cikakken sojan ruwa sannan ya damfari masu sana'ar POS bayan ya karbi kudi daga wurinsu.

"Nasiru Ahmed yana sanya kayan sojojin ruwa ne, ya je wurin masu sana'ar cire kudi (P.O.S) a wurare daban-daban a cikin karamar hukumar Karu da sunan yaje cire kudi, sai ya tura musu sakon shigar kudi na bogi ta wayar salula ya karbe musu asalin kudi." Ma'ana dai madamfari ne.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba