• Yan kungiyar IPOB sun kashe sojojin Najeriya biyu yayin wani artabu
  • Sai dai yanzu haka sojojin najeriya sun bi sawun yan IPOB din don karkade su
  • Kisan sojojin na nuna cewa kalubalen tsaro a yankin Kudu maso gabas ka iya yin nisa.
Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da harbe wasu dakarunta biyu a ranar Talata a jihar Enugu, yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, shine ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba cewa an kashe sojojin biyu a yayin artabun da aka yi tsakanin sojoji da wasu mambobin kungiyar (ESN), bangaren kungiyar masu rajin kafa Biafra, (IPOB) ).

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya, suna fatirol

Birgediya Janar Nwachukwu, yace lamarin ya faru ne a garin Adani da ke karamar hukumar Uzo-Uwani a jihar Enugu.

“An tura sojoji zuwa yankin domin su bincike 'yan bindiga a garin Adani a karamar hukumar Uzo-Uwani ta jihar Enugu, sun dakile harin bindiga na ESN a shingen binciken Iggah / Asaba a ranar Talata.

“Abin takaici, a yayin gumurzun fadan da ya barke, sojoji biyu sun rasa rayukansu.

"Sojojin Najeriya a halin yanzu suna kan bin sahun masu aikata laifin," in ji shi.

Birgediya Janar Nwachukwu ya tabbatar wa al'umma irin himmar da Sojojin Najeriya ke yi na samar da isasshen tsaro tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro.

Ya kara da cewa "Muna kuma yin kira ga jama'a da su ba da himma ga jami'an tsaro ta hanyar bin doka da kuma samar da bayanai masu amfani a kan 'yan bindigan da suka tsere.


Kisan sojojin na nuna cewa kalubalen tsaro a yankin Kudu maso gabas na iya yin nisa.

Yankin a baya-bayan nan ya sha fuskantar munanan hare-hare kan hukumomin tsaro da cibiyoyin jama'a kamar dakunan kotu, gidajen yari, da ofisoshin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta.

IPOB, wacce gwamnatin Najeriya ta haramta, ta sha musanta cewa tana da hannu a kashe-kashen da ake yi a yankin.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba