Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kaiwa wannan sanannen mai fafutukar kafa kasar Oduduwa, Sunday Igboho hari a ranar alhamis a garin Ibadan.

Mataimakinsa na musamma a sashen kafafen sada zumunta, Olayomi Koiki ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Yace: "Yan bindigar masu sanye da kakin sojoji sun kai masa harin ne da misalin karfe 1 na safe.

Ya kuma bayyana cewa, Igboho yana cikin gidansa lokacin da lamarin ya faru.

Koiki ya kara da cewa, motarsa kirar G-wagon da kuma Parado kirar SUV tare da wasu muhimman kayayyakin gidansa kamar tagogi da kayan ado duka 'yan bindigar sun lalata su.

Kalli hotunan motocin da suka sha alburusai a gidan Sunday Igboho.

Sunday Igboho

Gidan Sunday Igboho

Motar Sunday Igboho

Motar Sunday Igboho

Yace: "An ga was kofofi da alburushi ya huhhuda a jikin motocin, sannan jinin mutane ya zuba a tsakar gidan na Igboho".

Sai dai har yanzu, rundunar 'yan sandan jihar ba su ce kanzil ba game da harin.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba