Jiya aka fara haska shirin nan na gasken-gaske mai taken Big Brother Naija Season 6, cikin sa'a a wannan karon an samu daya daga cikin 'yan arewa ya samu nasarar zama jarumi a wannan shiri.

Yusuf Adamu Garba
Yousef Garba, Jos

Shin ko waye menene tarihin shi wannan jarumi a takaice? A cikin wannan takaitaccen rubutu za mu wallafa cikakken tarihin Yusuf Garba Adamau (Yousef Garba), jarumin BBNaija Season6.

Waye Yusuf Garba Adamu?

Haifaffen garin Jos ne, dake jihar Filato. An haife shi a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 1992 a garin Jos.

Gidansu ya hada da Mahaifinsa, Mahaifiyarsa da kuma 'yayunsa mata guda 2, sai yayunsa maza guda uku, kuma shine auta (sha mama) a cikinsu.

Mahafinsa dan Najeriya ne, mahaifiyarsa kuma Shuwa Arab (Balarabiya) ce.

Yayi kammala karatun digirinsa a jami'ar Jos, ya karanci sashen Electrical Electronics.

 Baya ga haka shi din 'dan kwalliya ne da kwalisa wanda ya ci gasar UNIJOS a shekarar 2015 sannan ya ci gasar CARNIVAL KING wacce aka gudanar a Jos a shekarar 2018.

Yanzu haka Yusuf, na daya daga cikin jaruman shirin BBNAIJA SEASON 6, mai taken Shine Your Eyes.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba