Mayakan taliban sun yiwa wani dan kasar Afghanistan kisan gilla ta hanyar sare masa kai.

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, mutumin yana daya daga cikin yan kasar Afghanistan da suke yi wa sojojin kasar Amurka aikin fassara abinda 'yan ta'addan taliban din suka fadi daga harshen larabci zuwa turanci.

Yan Ta'addan Taliban
image source: the-sun.com

Yan ta'addan taliban din sun kame Sohail Pardis mai shekaru 32 a ranar 12 ga watan Mayu, bayan ya baro gidansa dake birnin Kabul a cikin motarsa yana kan hanyarsa ta dauko 'yar uwarsa daga wurin sallar idin karamar Sallah.

Kafin aukuwar lamarin, Pardis ya fada wa abokansa cewa 'yan taliban suna masa barazanar kisa saboda suna zarginsa da yiwa sojojin amurka leken asiri.

"Suna fada masa kai dan leken asirin amurkawa ne, kai ne idanun amurkawa, sannan kai kafiri ne, sannnan za mu kashe ka da kai da ahalinka." Kamar yadda abokinsa Abdulhaq Ayoubi ya fadawa CNN.

"Pardis na tsaka da tuki, ya ci karo da madakatar bincike ta 'yan taliban, ya yi kokarin tserewa amma 'yan taliban din suka bude wa motarsa wuta, suka fito da shi suka sare masa kai" Kamar yadda wasu 'yan kauyen kasar Afghanistan suka tabbatar.

Pardis, musulmin kasar Afghanistan, ya yiwa sojojin Amurka aiki na tsawon watanni 16 a matsayin mai fassara musu abinda 'yan taliban din suka fadi daga yaren larabci zuwa turanci.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba