Wasu fusattun 'yan sandan Mopol sun fatattaki Gwamnan Zamfara, Bello Mohammed Matawalle kan zarginsa da halin ko-in-kula da yake nuna musu ta hanyar rashin basu kyakkyawar kulawa.

Gwamna Matawalle
Gov Matawalle, Zamfara State

Lamarin ya faru ne a asibitin Ahmad Sani Yariman Bakura da ke Gusau, lokacin da mai girma Gwamna ya kai ziyara dakin ajiye gawa don ganin gawarwakin 'yan sandan Mopol 13 da 'yan fashin daji suka kashe yayin bata-kashi a kauyen Kurar-Mota, Kamar Hukumar Bungudu.

Kamar yadda jaridar PRNigeria ta ruwaito, daya daga cikin shaidun gani-da-ido ne ya tabbatar da aukuwar lamarin.

"Bayan gwamnan ya ziyarci jami'ai marasa lafiyar da suka tsira daga harin 'yan bindigar, Gwamnan ya wuce zuwa dakin ajiyar gawarwaki, sai dai kafin ya karasa suka yi kacibus da fusatattun 'yan sandan."

A cewar shaidar gani da idon, jami'an sun yi korafin cewa sun yi kiran neman agaji ba adadi, amma ba wanda ya taimaka musu, duk da cewa sun yi bata-kashi da yan fashin ba tare da isassun alburasai ba

'Yan sandan na Mopol, wadanda galibinsu maza ne sun caccabawa gwamnan maganganu marasa dadi, wadda ta kai har daya daga cikinsu ya kusa cakumar gwamnan, amma abokan aikinshi suka rike shi.

Sun kara zargin gwamnan da yin watsi da alawus dinsu sama da shekara guda duk da cewa sun bar iyalinsu dogon lokaci kuma babu wani wanda ke kula da su.

"Sun ce koda samun damar cire albashinsu matsala e garesu sakamakon kowanne lokacin suna cikin daji."

Da ma tsohon Gwamnan Jihar ta Zamfara, Ahmad Sani Yariman Bakura, wanda aka sawa asibitin sunansa, ya shawarci Gwamna Matawalle da kar ya kai ziyara dakin ajiyar gawarwarkin.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba