Jiya labari ya iske mu cewa jami'an Interpol na Kasar Benin republic sun cafke Sunday Igobo da matarsa Ropo a filin tashi da saukar jirage na Cadjèhoun a babban birnin kasar wato Cotonou.

Sai dai har yanzu Gwamnatin Najeriya ba ta kudunduno Sunday Igbohon daga Benin ba ta dawo da shi gida, don girbar abinda ya shuka.

Sunday Igboho

Duk da lauyansa ya bayyana cewa, lokacin da yayi waya da Igboho, Sunday Igboho na sharbar kuka wiwi sakamakon irin kamun ludayin da jami'an tsaron kasar ta Benin Republic suke masa.

Sannan lauyan nasa ya kara da cewa, matar Sunday Igboho mai suna Ropo itama tana sharbar kuka a wani cell din daban.

To kamar yadda muka yi bincike, mun gano cewa a ka'idar kundin tsarin mulkin kasar Benin Republic, hukuncin shekaru 22 ne ga dukkanin wanda aka kama da mallakar fasfon bogi.

Sai ga shi, Sunday Igboho an kama shi da fasfon karya na Kasar Benin Republic a lokacin da yake kokarin tserewa kasar Germany, mahaifar matarsa.

Bisa wannan hujja da dalili muke ganin, muddin Kasar Najeriya ta bar Sunday Igboho a kasar Benin Republic, to daure shi za su yi na tsawon shekaru ashirin da biyu.

In kuma mahukunta suka samu nasarar karbo shi daga Benin Republic to kai tsaye kotu za'a wuce da shi bisa zarginsa laifin da tada zaune tsaye da kuma yunkurin raba kasar Najeriya.

Tattarawa bincike: Abba Abdullahi Garba

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba