Dangote Cement

Kamfanin Dangote Cement Plc yace kamfaninsa na samar da tan miliyan shida na siminti a duk shekara wanda ke Okpella, jihar Edo, zai fara aiki nan bada jimawa ba

A watan Mayun da ya gabata, kamfanin ya ce zai ci gaba da bunkasa samar da kayayyaki domin magance bukatar kayyakin da kuma rage farashinsa.

Patrick Omokagbo, daraktan gudanarwa na masu ruwa da tsaki na kamfanin simintin Dangote, ya ce ana sa ran kamfanin zai bunkasa samar da siminti a fadin kasar ta Najeriya.

Ya bayyana hakan ne lokacin da Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo, ya ziyarci sabon wurin samar da simintin a ranar Alhamis.

Omokagbo yace jama'ar yankin Okpella sun bada gudunmawa wajen gina masana'antar, haka ma injiniyoyi, masu aikin fasaha da sauran mambobin al'umma da suka yi aiki har zuwa lokacin da aka kammala shi.

"A Najeriya, muna da yawan mutane sama da miliyan 200. Masu amfani da siminti a Najeriya basu da yawa. Har yanzu muna bukatar kara zage damtse domin tabbatar da siminti ya isa ga talakan talak." inji shi.

A sabon wurin samar da siminti, an samar da wata tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 60 (MW), wanda ya hade da babbar hanyar Benin zuwa Abuja tare da titin kilomita 7.5 da kamfanin ya gina.

A cewar wata sanarwa daga kamfanin siminti na Dangote, masana'antar ta yi daidai da shirin da Obaseki ke jagoranta na fadada tattalin arzikin jihar da jawo hankulan masu saka jari a bangaren masana'antu.

“Obaseki yana cigaba da fafutukar jawo masu zuba jari tare da saukakan dokokin kafa masan'antu a jihar, wanda hakan ya haifar da kafa wasu masana’antun, wadanda suka hada da matatun mai na zamani, kamfanonin sarrafa iskar gas, tashar jirgin ruwa, da sauransu, "sanarwar ta bayyana.

A farkon wannan watan, kafamin siminti na Dangote ya sayi karin manyan tirololi dubu 20 da tikitinsu a kan kudi dala miliyan 150 domin bunkasa zagayawar kayayyakinsa a fadin Kasar Najeriya.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba