Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana kudirinta na samar da lita dubu 50,000 ta madarar shanu kullum a fadin jihar.

Gwamnatin ta bayyana cewa tana da damar da za ta iya samar da akalla lita 50,000 ta madarar shanu a kullum ta hanyar cibiyoyin tattara madara 200 (MCCs) da ke jihar domin cike gibin bukatar madara a Najeriya.

Kodinetan ayyuka da shirin bunkasa kiwon makiyaya na jihar (KSADP) Alhaji Ibrahim Garba Muhammad ne ya sanar da hakan yayin ganawa da masu ruwa da tsaki a harkar kiwo a jihar da yammacin ranar Alhamis, game da gano wuraren da aikin zai kasance, wanda hukumarsa za ta aiwatar. 

Ya bayyana cewa bisa la'akari da bayanan kiddigar da suke da shi, kowanne reshe na MCC zai tattara akalla lita 250 ta madara a kowacce rana.

Ya kara da cewa adadin zai karu sosai, yayin da shirinsa na samar da kayan aikin wucin gadi zai fara ba da jimawa ba.

 "Wannan zai kara karfafa ne ta hanyar niyar da muka yi a cikin kananan tsare-tsaren samar da karin dabbobi, wanda zai samar da karin makiyaya ga shanu, wanda zai haifar da karuwar samar da madara". 

“Dangane da wannan, mun bayar da aikin tuntuba don tsarawa da kuma lura da MCCs. Manufar ita ce a taimaka wajen inganta abinci mai gina jiki ta hanyar shan madara da kuma rage asara mai yawa ta fuskar lalacewar madara ”.

 “Idan mun kawo MCC din kusa da al’ummomi, kungiyoyn samar da nona na fulani ba za su bukaci yin jigila zuwa wuri mai nisa ba don siyar da madararsu. Wannan shine dalilin da ya sa muke neman wuraren da suka dace don gina cibiyoyin ”. 

Alhaji Ibrahim ya bayyana cewa kowace MCC za ta hada da kayayyakin sanyayawa, kayan gwaji, tanki da bankin kiwo da sauran abubuwa, yana mai jaddada cewa za a gudanar da cibiyoyin ne ta wani kwamiti da ya hada da masu ruwa da tsaki a cikin al'ummomin, domin dorewar shirin. 

Abin da ya burge shi da hujjar gina MCC din shine ganin shugaban Miyetti Allah Cattle Breeders Association, reshen jihar Kano, Alhaji Husaini Umar, ya ba da gonar sa da ke ‘Yan Rutu, karamar hukumar Dawakin Tofa kyauta, don daya daga cikin cibiyoyin da za a gina. 

A halin yanzu, mahalarta taron sun gano kimanin wurare 287 a duk fadin kananan hukumomin 44 na Kano, don yiwuwar gina Cibiyoyin Tattara Madara. 

Masu ruwa da tsaki, duk da haka, sun ba da shawarar cewa al'ummomi su hada kai da kananan hukumomi da jihohi, don samar da wurare masu tsaro don gudanar da ayyukan, saboda kalubalen tsaro a wasu sassan kasar. 

Sun yi alkawarin hada kawunansu domin tabbatar da cewa ayyukan sun kai ga cin nasara, kuma an cigaba da yinsu don cigaban makiyayan jihar Kano.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba