Wasu 'yan bindiga sun sace matar mai fafutukar kafa kasar Oduduwa, Sunday Igboho bayan sun kai hari gidansa a ranar alhamis da safe.

Sunday Igboho

Farfesa Banji Akintoye, shugaban jagororin yanke hukunci na Yarabawa shi ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar mai taken, "Kasar Yarabawa: Sojojin Najeriya, tare da rakiyar 'yan ta'addan duniya da Gwamnatin Najeriya ta dauka haya sun kai hari gidan Sunday Igboho - Inji Akintoye."

Manajan watsa labarai na Farfesa Akintoye, Mista Maxwell Adeleye ne ya bayyana hakan ga menama labarai.

A wani bangare na sanarwar manema labarai sun bankado inda aka ce, "Maharan duk suna sanye da kayan sojoji kuma duk suna magana da yaren faransanci rangadadau."

"Yan Bindigar sun kashe mutum bakwai a cikin gidan, sannan suka tisa keyar matar Igboho da wasu da dama daga gidan."


Kamar yadda jaridar ta dailypost ta wallafa, wannan na zuwa ne kasa da awanni 72 kafin a shirya babbar zanga-zanga  a Jihar Legas, wanda Akintoye da Igboho za su halarta.

Har yanzu ba'a san takamaiman abinda ya faru ba kamar yadda Jami'in Hulda da Jama'a na 'Yan sandan Jihar, Olugbenga Ayo, ya kasa daga wayar manema labarai.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba