Wani mamakon ruwan sama, hade da iska, wanda ya kwashe kimanin sa'o'i uku a safiyar ranar Alhamis ya lalata wasu gidaje a cikin rukunin gidajen Kundila da ke daura da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, kan titin Zariyar a Jihar Kano.

Baya ga haka, gidaje da dama dake yankin suma wannan ambaliyar ruwa ta rutsa da su, lamarin da ya haifar da mummunar barna da ba za a iya tantancewa ba, wanda aka kiyasta akalla ya yi barna ta sama da Naira miliyan 60.

Ambaliyar ruwa a Kundila

Gidajen na Kundila na cikin wata babbar hanyar magudanan ruwa, wanda ke rarraba ruwa daga gidan Gwamnati, Tarauni, da Hotoro zuwa wata babbar magudanar ruwa wacce ke da harsuna biyu a titin Zariya.

A cewar wani mazaunin Estate din, Mustapha Haruna, ruwan saman na awanni bakwai ya haifar da asara ga mazauna unguwar, musamman wadanda gidajensu suka nutse kwata-kwata, da yawa daga cikin kadarorinsu sun salwanta, kamar talabijin, gado da gado da kayan kwalliya.

Mustapha ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su kawo musu dauki da kayayyakin tallafi.

Manema labarai sun yi kokarin jin ta bakin kwamishinan muhalli na Jihar Kano, Kabiru Gestso, domin jin ta bakinsa amma basu ci nasa ba.

Amma jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Sanusi Na’isa, ya ce ma’aikatar na sane da wannan mummunan iftila'i da ya fadawa al'ummar Kundila..

A cewarsa, jami'an ma'aikatar sun gudanar da bincike a yankin 'yan kwanaki kafin aukuwar ambaliyar, suna masu jaddawa mazauna wurin da lallai a share magudanan ruwa saboda gudun irin haka.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba