_Babban limamin masallacin gida rediyon otel, Yola ya bayyana kudinsa na tsayawa takar gwamnan adamawa

_Malam Abdulkadir ya bayyana kyawawan manufofinsa na tsayawa takarar

_Sannan ya bukaci al'ummar jihar da su saka shi a addu'a domin manufarsa ta ida nufi

Wani babban limami a Jihar Adamawa ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Adamawa a zabe mai zuwa.

Malam Abdulkadir Isah, shine babban limamin masallacin gidan talabijin din Jihar Adamawa (ATV) ya fito karara ya bayyana kudinsa na tsayawa takar gwamnan a zabe mai zuwa.

Malam Abdukadir Isah
Limami: Malam Abdukadir Isah

Haka kuma Malam Abdulkadir ya kasance limamin gidan rediyon otel dake a garin Yola, kuma yana wato ainihin bada fatawar addini.

Kamar yadda jaridar Aminiya ta wallafa, malamin ya bayyana kudinsa ne yayin zantawa da menama labarai a ranar laraba, 2 ga watan yuni, a garin Yola.

Ya nemi al'umma su saka shi a addu'a, inda yake hakika manufarsa ta wannan fitowa takara za ta faratawa al'ummar jihar rai ba tare da wani banbancin addini ba, da kuma kawo canjin da ake bukata.

Sannan malam ya kara da cewa: "Na zaga  wasu daga cikin kasashen duniya, na ga yadda malam talaka yake da daraja."

"Kuma shi ya dauki wannan takarar tasa a matsayin zaiyi ibada ne, bi-ma'an abinda Allah zaiyi sakayya da shi."

"Sannan na sani ba dukkan malami, limami ko almajirin ilimi ne zai iya fitowa ba a wanna fagen don gudun maganganun masu magana".

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba