Dubun wasu 'yan fashi da suka saci wata mota ya cika yayin da aka cafke su a wani asibiti bayan sun yi hatsari a hanyar Ode Remo da ke arewacin Karamar Hukumar Remo ta Jihar Ogun.

Wadanda ake zargin sun kwace wata mota kirar Toyota Camry ta hanyar yin barazana ga mai ita da bindiga a jihar Ondo, suna kan hanyarsu ta zuwa Lagos ne suka yi hatsarin, kamar yadda jaridar dailytrust ta ruwaito.

Barayin mota
Barayin mota ada akan kama a ogun

Jami'an 'yan sanda reshen Karamar Hukumar Ode sune suka tseratar da mutum uku da ke cikin motar ta hanyar kaisu asibiti cikin gaggawa domin ceton rayukansu.

A cewar Abimbola Oyeyemi, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Ogun, wadanda ake zargin suna karbar magani a lokacin da DPO na reshen Ode Remo, Fasogbon Olayemi, ya samu labarin cewa motar da ta yi hatsarin an kwato ta ne da bakin bindiga daga hannun mai ita.

Ya ce da sauri DPO ya ba da umarnin cewa a tsare barayin a asibiti.

“Mai motar da ya zo daga jihar Ondo ya bayyana cewa wasu gungun mutane biyar ne sanye da kayan‘ yan sanda suka tare shi a kan hanya, kuma an yi amfani da bindiga an ciro shi daga motar an dauke motar, ”In ji shi.

Oyeyemi ya bayyana cewa daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Emeka John daga baya ya mutu a asibitin sakamakon hatsarin.

Kwamishinan 'yan sanda, Edward Ajogun, nan da nan ya ba da umarnin a tura sauran mutum biyun, Sunday Emmanuel da Idris Ibrahim, zuwa sashin binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar don gurfanar da su a gaban kuliya manta sabo.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba