Wasu mahara sun kai hari wani masallaci a Osogbo, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutum daya tare jikkata wasu da dama daga cikin masallatan.

Kamar yadda jaridar ThePunch ta ruwaito, an harbe wani mai suna Moshood Salahudeen, yayin da sauran mutum tara suka samu raununka bayan wasu mahara sun kai hari a gaban wani masallaci a Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci

Shugaban maharan da mabiyansa an bayyana cewa sun zo wucewa ne ta harabar masallacin lokacin ana tsaka da sallah a karkashin rufin kusa da masallacin a ranar Lahadi, lokacin da lamarin ya faru.

An kuma bayyana cewa, maharan sun lalata dukkanin tagogi da kofofin masallacin yayin kai harin.

Babban Limamin Masallacin, Alhaji Qouseem Yunus a wata tattaunawa da aka yi da shi a ranar litinin ya ce, babu wani sabani da ya shiga tsakaninsu da maharan.

Ya kuma kara da cewa, rundunar maharan da farko ta wuce ta yankin ba tare da ta farwa masu ibadar ba.

Ya ce, “Muna zaune a wajen masallacinmu, muna yin addu’o’i na musamman a ranar Lahadi lokacin da maharan suka far mana, kuma 'Yan sanda hudu suna tare da su."

“Da farko sun wuce ta inda muke, daga baya suka dawo inda muke zaune suka fara jifarmu da duwatsu.

Kana daga baya suka fara harbin mu tare da saranmu da adduna.

An kashe mutum daya daga cikinmu, mun dauki gawar zuwa Asibitin Koyarwa na UNIOSUN. 

Sauran mutane tara da suka samu raunuka na karbar magani a wasu asibitocin da ke Osogbo. ”

Sai dai da manema labarai suka yi kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Osun, Yemisi Opalola, har yanzu basu samu wani bayani daga garesi ba.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba