Bidiyon wani lakcara ya karade kafafen sada zumunta inda aka ganshi yana korar dalibai maza daga ajinsa saboda askin banzan da ya gani a kansu kamar yadda shafin InstagBlogNaija ya wallafa a shafin Instagram.

Lakcara ya kori dalibansa akan askin banza
Lakcara ya kori dalibansa akan askin banza

Malamin dai ana tunanin Shugaban daya daga cikin sashe (HOD) ne a jami'ar tarayya ta Jihar Oyo.

A cikin bidiyon an ga malamin yana hantarar daliban tare da musu tsawar su mike su fice masa daga cikin ajinsa.

Lamarin dai ya faru a ranar Laraba, ashirin da uku ga watan mayun 2021.

Kalli bidiyon:


Daga cikin daliban wasu an gansu a askin banza na Punke da kuma Afro a kansu.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba