Gwamnatin Najeriya ta amince za ta bude kafar twitter kowa ya ci gaba da amfani da ita, amma bisa wasu sharudda kwarara guda uku.

Ministan bayanai da al'adu, Lai Mohammed ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar bayan kammala zama da masu baiwa shugaban kasa shawara.

Muhammadu Buhari, Jack Dorsey
Hoto: Mbuhari @Facebook | Jack Dorsey @Twitter

Kamar yadda hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya bayyana, gwamnati ba za ta janye takunkumin kullen ba har sai kamfanin twitter:

  1. Yayi rajista da gwamnatin Najeriya
  2. Gwamnatin Najeriya ta bashi lasisi
  3. Sannan kamfanin zai rinka bin dokokin da gwamnati ta gindaya masa.

Wadannan sune sharrudan da gwamnatin Najeriya ta gindayawa kamfanin twitter, kafin twitter ya dawo aiki a fadin Najeriya.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba