Rundunar sojin saman Najeriya tayi ruwan bama-bamai akan wasu 'yan bindiga a kusa da garin Genu na jihar Neja.

Ruwan bama-baman yayi sanadiyar mutuwar da dama daga cikin 'yan bindigar.

PRNigeria ta ruwaito cewa wasu daga cikin shanun da 'yan bindigar suka sato suma harin ya rutsa da su.

Helikwaftan Sojoji
Naf Alfa Jet | Hoto: Nigerian Air Force

Jirgin da ya kai harin sunansa NAF Alfa Jet, kuma ya taso ne daga sansanin sojoji a jihar Katsina.

Wani shaidar gani da ido yace; "daya daga cikin bama-baman ya fada kan wasu tawagar 'yan daurin aure a wani kauye kusa da Genu."

"Munga wani karamin jirgi yana jefo bama-bamai nesa da inda 'yan bindigar suke sannan daya daga cikin ababen fashewar ya fada a cikin taron 'yan daurin aure a kauyen Argida."

"Biyu daga cikin 'yan kauyen sun rasa rayukansu, sannan mutane da dama wadanda baki ne sun samu raunuka."

Yayin da PRNigeria ta tuntubi mai magana da yawun rundunar sojin saman Najeriya, Kwamared Edward Gabkwet yace, anci nasara yayin gudanar da harin.

"Bamu samu wani bayani ba akan mutanen da suka jikkata, manufarmu akan 'yan bindigar dake yankin Genu ne, bayan mun samu rahoto fasaha akan yan bindigar na kokarin yin ta'addanci wa al'umma."
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba