Sojojin Najeriya karkashin rundunar Operation Hadin Kai sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram-Iswap da yawa, sannan biyu daga cikin jami'ansu sun rasu.

Sojojin sun fatattaki dimbin 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP lokacin da suka yi artabu da su a yankin Bula Yobe da ke garin Banki, karamar hukumar Bama ta Jihar Borno.

Sojoji sun kashe yan boko haram | Hoto: prnigeria.com

Kamar yadda PRNigeria ta ruwaito, wani jami'in leken asiri ya tabbatar da cewa 'yan ta'ddan sun yi yunkurin kai hari kan wata rundunar sojoji a dai-dai lokacin da sojoji 21 na rundunar Operation Hadin Kai suka fatattake su a artabun da ya dauki tsawon sa'o'i biyu.

Majiyar ta ce: "'yan ta'adda wadanda akae zargin sun fito ne daga dajin Sambisa a kan manyan motoci guda shida dauke da bindigu sun tunkari yankin daga bangarori da daban-daban lokaci guda son yin barna, amma sai gwanayen sojojin suka musu rubdugu."

"'Yan ta'addan sun matukar razana matuka, da dama daga cikinsu suka ji munanan raunuka, ruka ranta a na kare suka bar makamai (AK 47) da dama da alburusai da suka hada har da bindigar harbo jirgin sama."

Sai dai abin takaici jaruman sojoji guda biyu sun rasa rayukansu yayin artabun.

Tuni dai rundunar ta Operation Hadin Kai ta marawa sauran 'yan ta'addan da suka gudu baya cikin dajin Sambisa don karasa karkade su.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba