Rundunar yan sanda Jihar Adamawa ta bayyana cewa; jami'anta na karamar hukumar Song sun yi nasarar ceto wani matashi dan shekaru 22 mai suna Usman Manu daga hannun masu garkuwa.

Wannan jawabi ya fito ne jiya laraba, daga bakin mai magana da yawun rundunar 'yan Sandan Jihar, DSP Sulaiman Ngoruje a wata sanarwa da ya fitar.

Aliyu Adamu Alhaji
Aliyu Adamu Alhaji da 'dan Garkuwan da aka kama

DSP Ngoruje yace sun jikkata daya daga cikin masu garkuwan.

Sannan ya kara da cewa masu garkuwa sun bukaci Naira miliyan 3 kudin fansa, bayan sun gudanar da ta'addancinsu tsakanin 1 zuwa na daren ranar 28 ga watan mayu.

"Kamar yadda muka samu rahoto, Mutum hudu dauke da makamai sun mamaye gidajen kauyen Gola, sun musu barazana da bakin bindiga sannan suka yi garkuwa da Usman Manu mai shekaru 22."

"Masu garkuwar daga baya sun kira waya, sun bukaci miliyan 3 kudin fansa, sannan sunce a kai musu kudin a wani wuri kuda da dutsen Zumo."

"Kwamishinan 'yan sanda jihar, Aliyu Adamu Alhaji, nan take ya tura rundunar iyan sandan karamar  Gola, tare da 'yan kato-da-gora domin su kubuto da Usman Manu."

"A kokarin masu garkuwar na tserewa, suka fara harbo wa dakarunmu alburusai, sai dai bayan dakarunmu sun maida martani sun samu nasarar jikkata daya daga cikin masu garkuwar, sannan suka kubutar da shi Usman Manu."

DSP Ngoruje ya kara da cewa: "Kwamishinan 'yan Sandan jihar ne ya tura jami'an karamar hukumar Song da yan kato-da-gora domin su kubutar da wanda aka yi garkuwar da shi."

Ya kuma umarci jami'an da su bi bayan 'yan gaskuwar, kana ya ja hankalin al'umma da su ci gaba da kai rahoton duk wani motsi da basu yarda da shi ba a yankunansu.

DSP Nguroje ya kuma yiwa al'ummar yankin alkawarin goyon bayan rundunar 'yan sanda domin kare rayuwarsu da dukiyoyinsu.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba