_Jam'iyyar PDP ta bukaci gwamnan jihar Imo yayi murabus

_Haka-kuma jam'iyyar ta bukaci gwamnatin jihar ta sa ayi kwakkwaran bincike akan kisan Ahmed Gulak

_Shugaban jam'iyyar yace suna ankare da kama matasa da kasheshu da soji keyi

Jam'iyyar PDP reshen Jihar Imo ta bukaci gwamnan jihar Hope Uzodinma da ya yi murabus daga kan karagar mulki saboda hauhawar matsalar rashin tsaro a fadin jihar.

Jaridar Punch ce ta ruwaito wannan labarin.

A taron manema labarai Owerri, babban birnin jihar, Shugaban jam'iyyar ta PDP, Charles Ugwu yace da alamu gwamnan bashi da amsar da zai bayar akan kashe-kashen da ke faruwa a jihar.

Hope Uzodinma
Hoto: @Hope_Uzodinma1 Source: Twitter

Har-ila-yau, jam'iyyar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta sa ayi kwakkwaran bincike akan kisan Ahmed Gulak da aka yi a ranar Lahadi da safe.

"Gwamna Uzodinma a matsayinsa na shugaban tsaron jihar ya gaza wajen bada kariya ga rayuwar al'ummar jihar da kayayyakin Gwamnati."


"Wannan bayyanannen abu ne, gwamnatin APC ta gaza kare al'ummar jihar da dukiyoyinsu in aka yi duba da irin abubuwan da ke faruwa a fadin jihar."

Shugaban jam'iyyar yace jam'iyyarsu ta adawa tana ankare da karuwar kama matasa da kashesu da sojoji keyi.

Ugwu ya kara da cewa jam'iyyar PDP ta matukar damuwa kwarai da gaske da irin cin kashin da akewa matasa a jihar, da kuma kone ofishin hukumar zabe da kuma ofisoshin 'yan sanda.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba