Hukumar tsaro ta  NSCDC a ranar Laraba ta sanar da tura jami’ai mata zuwa makarantu a fadin kasar don kare dalibai da malamai daga yawaitar harin da 'yan garkuwa ke kaiwa kamar yadda PremiumTimes ta ruwaito.

Jami'an NSCDC Mata
Jami'an NSCDC mata

Kwamanda Janar na Hukumar, Ahmed Audi, ya ba da umarnin tattarawa tare da horar da jami'ai mata na tsawon wata guda domin samar da kwararrun jami'ai a dukkanin Jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja don wannan manufa.

Ya kuma kara da cewa tura jami'an na cikin daga wani shiri na tabbatar da samar da tsaro ga makarantu wanda Ministan Ma'aikatar Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya bayar da umarnin ayi.

Yace "Ministan ya bashi urmanin ujila akan ya samar da jam'ai wadanda za su kawo karshen matsalar satar dalibai  a makarantu a fadin Kasar."

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba