_ Masarautar Karaye ta nada Alh. Saleh Musa Kwankwaso Hakimin Karaye

_ Masarautar ta kuma kara nada shi Makaman Karaye biyo-bayan nadin Hakimin da aka yi masa

_ Tuni dai masarautar ta mika da sunansa domin majalissar dokokin Jihar Kano ta amince da shi.

Majalissar Masarautar Ƙaraye ƙarƙashin jagorancin mai Martaba Sarkin Ƙaraye Alh. Dr Ibrahim Abubakar III ta amince da Saleh Musa Kwankwaso a matsayin Hakimin Ƙaramar Hukumar Madobi.

Ha-ila-yau Masarautar ta Ƙaraye ta ƙara nada Alh. Saleh Musa Kwankwaso Makaman Masarautar Ƙaraye.

Masarautar Ƙaraye ta nada Saleh Musa Kwankwaso Hakimin Madobi, Makaman Ƙaraye.

Wannan sabon nadi ya biyo bayan rasuwar marigayi Musa Saleh Kwankwaso mahaifi ga Tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya (Rabiu Kwankwaso) da Saleh Musa Kwankwaso.

Rabiu tare da Sale Musa Kwankwaso

Kamar yadda muka samu labari ta bakin Salihu Tanko Yakasai (Dawisu), Sabon Hakimin Madobin shine dagacin garin Kwankwaso kuma ya daɗe yana yi wa garin da al'ummar garin Hidima.

Wanda hakan yasa ya cancanta ya gaji mahaifin nasa marigayi Musa Saleh Kwankwaso.

Yanzu haka dai Majalissar Masarautar Ƙaraye za ta mika wa Gwamna Ganduje rubutaccen bayani akan naɗin sabon hakimin domin buƙatar amincewarsa.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba