_Mai babban daki, Maryam Bayero ta rasu

_Ta rasu a wani asibiti a birnin Cairo, Egypt

_Ita ce mahaifiyar Aminu Ado da Nasiru Ado Bayero

Labari da dumi-duminsa, yanzu muka samu labarin rasuwar Maryam Bayero, mahaifiyar Sarkin Kano Aminu Ado.

Mamaciyar, wadda ita ce mahaifiyar Sarkin Bichi, Nasiru Bayero ita ce tsohuwar mace mai takaba, cikin matan marigayi Ado Bayero.

Iyalan Masarautar Sarkin Kano sun tabbatar da labarin mutuwar Maryam Bayero wa gidan Jaridar Daily Nigerian.
image source: DailyNigerian.com

Maryam Bayero ta rasu ne ranar Asabar da safe a wani abitin birinin Cairo, Kasar Egypt.

Ana kiranta da Mai Babban Daki, ma'ana mahaifiyar Sarki.

Karin bayani na nan tafe..

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba