_ Kotu ta bayar da belin Mahadi Shehu amma bisa wasu sharudda

_ Jaridar Dailytrust ce ta ruwaito labarin

_ Gwamnatin Jihar Katsina karkashin Gwamna Aminu Bello Masari ce ta maka shi a karar.

Kotun tarayya da ke birnin Kano ta bayar da belin Mahdi Shehu beli biyo-bayan ƙin amsa laifi guda shida da Gwamnatin jihar Katsina ke zarginsa da shi.

Facebook/Mahadi Shehu Katsina

Kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito cewa; Mai shari'a Justice Lewis Allagoa ya bayar da umarnin kada a saki Mahdi har sai ya cika sharuɗɗan belin.

Kotun ta Federal High Court ta bayar da belin na Mahdi ne akan Naira miliyan 10, sannan dole sai wani mazaunin Jihar Kano mai dukiya (gida) ya tsaya masa.

Daga ƙarshe dai kotun ta dage ƙarar ne zuwa ranar 19 ga watan Mayu na shekarar 2021 da muke ciki.

Gwamnatin Jihar Katsina dai ta maka Shehu Mahdi a kotu ne biyo-bayan zargin Gwamna Aminu Bello Masari da Almundahana da Almubbazaranci da dukiyar al'umma.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba