Babbar kotu ta kasar Afirka ta kudu ta yanke wa tsohon shugana kasar, Jabo Zuma hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni 15, babu beli.

Kotun ta yanke masa hukuncin ne sakamakon raina kotun da yayi ta hanyar kin yin biyayya da ya yi a gaban masu binciken cin hanci da rashawa da ake tuhumarsa akai.

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma

Kamar yadda alkalin kotun, Sisi Khampepe ya bayyana, "Kotun ba za ta iya yin komai ba face ta yanke wa  Zuma hukunci sakamakon aikata laifin raina kotu".

A kasar ta Afirka ta Kudu, ana tuhumar Zuma, mai shekaru 79, da laifin yin wasarere tare da baiwa barayi damar wawure dukiyar kasa, yayin da ya kwase shekaru tara yana mulki.

Alkali Khampepe yace "Irin wannan nuku-nukun da bijirewa ya sabawa doka, kuma za'a hukunta shi".

"Ba ni da wani zabi face na daure Zuma a kurkuku, tare da fatan yin hakan zai aika da kurman sako don tabbatar da adalci".

"Sannan kotun ta umarci tsohon shugaba Zuma da ya mika kansa cikin kwanaki biyar".

Kwamitin binciken tsohon shugaban kasar yana karkashin jagorancin Mataimakin Babban Mai Shari’a Raymond Zondo.

Amma sau daya kawai tsohon shugaban ya bayar da shaida, a cikin watan Yulin shekarar 2019, kafin a tafi yajin aikin kwanaki, bayan haka ya zargi Zondo na hukumar da nuna son kai.

Sannan ya yi watsi da gayyata da yawa don sake bayyana a gaban kuliya, yana mai ba da dalilai na rashin lafiya da shirye-shiryen sake shari'ar cin hanci da rashawa.

Tsohon shugaban kasar ya sake gabatar da kansa a taƙaice a cikin watan Nuwamba amma ya fice daga dakin binciken kafin a yi masa tambayoyi, kuma Zondo ya nemi Kotun ta sa baki.

Mafi yawan kudaden da hukumar ta binciko sun hada da 'yan uwa maza uku daga wani attajirin dan kasuwar Indiya, Guptas, wadanda suka sami kwangilar gwamnati mai tsoka kuma har ma ana iya zaben ministocin.

Zuma na fuskantar tuhume-tuhume 16 daban-daban na zamba, damfara da kuma yin damfara da suka shafi sayen jiragen yaki na 1999, jiragen sintiri da kayan sojoji daga kamfanonin makamai biyar na Turai kan dala biliyan 30, sannan kwatankwacin kusan dala biliyan 5.

A lokacin siyan, Zuma ya kasance mataimakin shugaba Thabo Mbeki.

Ana zarginsa da karbar cin hanci da ya kai zunzurutun kudi miliyan hudu daga daya daga cikin kamfanonin, babban kamfanin tsaron Faransa Thales.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba