Jiragen yakin Sojojin saman Najeriya sun yi ruwan bama-bamai kan 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP a Jihar Borno tare da kone motocinsu na yaki.

Kazalika jiragen yakin ana tsammanin sun yi nasarar hallaka kwamandan 'yan Boko Haram din mai suna Modu Sulum tare da 'yan ta'addan da ke tare da shi.

Lamarin ya faru ne a garin Lamboa, Karamar Hukumar Kaga, Jihar Borno, kamar yadda jaridar PRNigeria ta ruwaito.

Helikwaftan Sojoji
Naf Alfa Jet | Hoto: Nigerian Air Force

Jirage masu saukar ungulu guda biyu ne suka yi ruwan bama-baman.

Modu Sulum shine wanda ya dauki nauyin lalata karafan high tension da ke kawai Jihar Borno wuta, sannan shine ya kaddamar da hari akan matafiya a garin Auno da Jakara.

'Yan ta'ddan dukansu na dauke da motocin yaki takwas sannan sun mamaye garin Damboa, kuma suna shirin sake kai sabon farmaki a garin Mainok jiragen masu saukar ungulu suka kaddamar musu.

Kamar yadda muka samu rahoto sama da mutum sha biyu daga cikin 'yan ta'addan sun bakunci lahira bayan ruwan bama-baman da jiragen suka yi akan su.

Da aka tuntunbi mai magana da yawun rundunar sojin saman Najeriya, Edward Gabkwet ya tabbar da nasarar da jiragen yakin suka samu.

Yace: "Eh, an samu nasara a harin, jiragen sun yi nasarar tashin 6 daga cikin motocin tare da kashe 'yan ta'adda masu yawa."

"A halin yanzu sojojin kasa tare da wasu jami'an mu sun dira wurin domin duba irin nasarar da aka samu."
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba