Hukumar tsara jarabawar shiga jami'a (JAMB) a ranar juma'a, ta ce daliban da suka zauna jarabawar UTME tsakanin ranakun 19 da 22 ga watan Yuni, yanzu za su iya duba sakamakon jarabawar su.

Jamb Logo

Za su yi amfani da gajerun lambobi ne wadanda za su latsa a wayoyiyinsu su tura sako ga lambar 55019.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar wacce shugaban harkokin jama'a da yarjejeniya, Fabian Benjamin ya sa wa hannu, ya yaba da karbar lambar shaidar dan kasa (NIN) da Gwamnatin Najeriya ta shigar cikin jarabawar.

Ya kuma bayayana hada jarabawar ta Jamb da NIN a matsayin hanya wacce ta kawo raguwar munanan ayyuka a yayin jarrabawar.

Ya ce; "Kwamitin ya lura da gamsuwa cewa amfani da NIN (Lambar Shaida ta Kasa) ya taimaka wajen magance yin magudin jarabawar,  wanda ba'a taba samun gagarumin raguwar magudin jarabawa ba kamar wannan tunda aka fara CBT a Najeriya.

Mista Benjamin, duk da haka, ya kara da cewa Hukumar JAMB za ta ci gaba da nazari kan “hotunan CCTV da sauran na’urori domin gano mummunar dabi’a yayin jarrabawa.”

Kakakin JAMB din ya kuma bayyana cewa a yanzu haka ba'a saki sakamakon gaba daya ba saboda bincike da ake yi.

Sannan ya yi barazanar cewa, “hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen janye sakamakon duk wanda aka gano ya aikata wani nau’i na rashin da’a a jarrabawar.”

JAMB ta fara jarabawar da ke gudana a ranar 19 ga Yuni kuma ta ce za ta ci gaba har zuwa 3 ga Yuli.
Labari na baya Labari na Gaba