Jam'iyyar PDP ta gargadi gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, akan sauya sheka daga jam'iyyar zuwa APC, inda PDP tace yana kasadar rasa kujerarsa.

Mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, shi ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Bello Matawalle
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle

Ya ce babu wata doka da ta baiwa gwamnan damar tsallakawa zuwa APC ko wata jam'iyya, tunda doka ta bashi damar fita daga jam'iyyar da yake ciki ta hanyar kada kuri'a. 

Kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Jam'iyyar ta kuma gargadi 'yan majalissar dokokin jihar Zamfara da cewa, kar su yarda a tursasasu su rasa kujerunsu, domin kundin tsarin mulki ya hana 'yan majalissu barin jam'iyyar da suke ciki bayan sun zama zababbu.

PDP ta mayar da wannan martani ne kan wani shiri da Gmamna Matawalle ya yi na sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

A wani labarin daban, jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya ba da shawara Matawalle ya bar PDP ya koma APC.

Mai taimakawa shugaban kasar a kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad ya bayyana cewa Matawalle ya bar PDP zuwa APC, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

"Jam'iyyar PDP tana gargadi ga Bello Matawalle da ya sani, shirye-shiryen da yake na barin jam'iyyar daidai ya ke da barinsa ofis.

"Domin babu wata doka da ta bashi damar sauya sheka zuwa wata jam'iyya daban ba tare da amincewar jam'iyyar da yake ciki ba, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar." Inji PDP a cikin sanarwar da aka fitar yayin taron manema labarai.


Idan har Matawalle ya koma APC, to zai zama gwamna na uku na PDP da ya koma APC a cikin watanni bakwai da suka gabata.

Sauran gwamnoni biyu da suka yi hijira daga jam'iyyar zuwa APC sun hada da, gwamnan Ebonyi da Kuros Riba.

Yin hijira gwamnoni da sauran zababbun jami'ai daga wannan jam'iyya zuwa waccan, sanannen abu ne a siyasar Najeriya, kuma babu wani gwamna da ya taba rasa kujerarsa a baya saboda ya canza jam'iyya.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba