_Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta aike da wata takardar kashedi ga wani gidan Rediyo akan kalmar "Black Friday".

_ Hukumar ta Hisbah ta bayyana cewa kalmar Black Friday barazana ce ga tsaro da zaman lafiyar al'ummar Jihar Kano, sakamakon kaso 99 na mazauna jihar Musulmai ne.

Mecece Kalmar Baka Juma'a?

"Ita dai wannan rana ta baƙar juma'a kan kasancewa ranar juma'a ta hudu a watan Nuwambar kowacce shekara, inda ƴa kasuwa kan zabtare farashin kayayyaki ga abokan cikikinsu gabannin Bikin Kirsimeti."

Wannan gargadi dai cikin wasika Hukumar Hisba ta aika shi ne ga Manajan Gidan Rediyon Cool FM dake Birnin Kanon Dabo.

Manema labari sunyi koƙarin jin ta bakin Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, sai dai Abubakar Ali wani jami'in Hisbah suka samu damar tattaunawa da shi.

Abubakar Ali ya bayyana cewa: mafi akasarin mazauna Jihar musulmai ne wadanda ke kallon ranar Juma'a a matsayin rana mai tsarki.

Kazalika Ali ya kara da cewa: akan haka tashar Rediyon Cool FM ta daina amfani da kalmar Black Friday ba tare da bata lokaci ba.

To mai karatu, ga dai abinda wasikar ta Hukumar Hisbah ta ce:

"Muna bayyana damuwa kan ayyana Juma'a a matsayin Black Friday, kuma ya kamata a fahimci yawancin al'ummar Kano Musulmi ne da suka ɗauki Juma'a babbar rana."

"Don haka Hisbah na son a daina kiran Juma'a Black Friday cikin gaggawa, kuma a kula cewa jami'an hukumar za su kasance a girke domin kula da lamura domin gudun afkuwar kowani irin abu na rashin da'a da kuma wanzar da zaman lafiya da aminci a jihar. Muna fatan alkhairi."

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba