Tsohuwar tauraruwa kuma jaruma a masana'antar fina-finan hausa ta Kannywood, Fati Baffa Fagge, wacce aka fi sani da Fati Bararoji a wata tattaunawarta da jaridar Dimokuradiyya ta bayyana cewa ita fa har yanzu ba ta yi tsufan da za'a dena yayin ta ba a Kannywood.

Ta kuma bayyana cewa, har yanzu ana damawa da ita tamkar lokacin da take kan ganiyar kuruciyarta.

Jaruma Fati Bararoji

Da ake tambayarka ko me yasa yanzu irin su da suka dade ba sa motsi, ko dai sun barwa na baya ne wadanda suka shigo harkar ta fim din yanzu, duba da yadda su suka ci zamaninsu a lokacin baya.

Sai dai jaruma Bararoji ta yi azamar ba da amsa "ba wani lokaci da za'a ce sun ci a baya, kuma yanzu sun zo suna cin na wasu, don haka yanzu ma lokacin su ne." Inji ta.

Da ake tambayarta dalilin da ya ba'a ganinta yanzu? sai ta ce "da ba'a ganina ba wai na daina fim bane, wasu harkokin kasuwancin da nake ne suka sa ba'a ganii na, don kada na karbi aiki ya zama ban samu zuwwa ba."

"Amma da yake yanzu ina samun lokaci ai gashi ana gani na, don haka babu wani daina yayin mu da aka yi, kuma har yanzu muna cin lokacin mu."

Daga karshe jaruma Fati Bararoji ta yi kira ga daukacin masoyanta da su ci gaba da kallon dukkan fina-finan da za su fito nan gaba, domin za su ci gaba da ganin ta musamman a fina-finan da ake haskawa a tashoshin talabijin.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba