_ Gwamnan Kaduna ya sa an rushe Otal din da aka shirya za'ayi dabdalar cikin dare

_ Jami'an tsaron jihar Kaduna sun yi nasarar kama wadanda suka shirya dabdalar

_ Tuni dai yan sanda suka dakile dabdalar da aka shirya a jihar ta Kaduna.

Rahotanni daga Jihar Kaduna sun tabbatar da cewa, Gwamna Nasir el-Rufa'i ya bada umarnin rushe gidan da aka shirya yin dabdalar lalatar nan ta cikin dare wato Sex Party.

Idan mai karatu ba manta ba: Kwanaki hudu da suka gabata ne dai aka kama wasu matasa da suka shirya dabdalar (sex party) wacce za'ayi a Kaduna.

Twitter/Nasir el-Rufa'i

Jami'an tsaron Jihar Kaduna sunyi nasarar daƙile wannan taro lalata tare da damƙe waɗanda suka shirya dabdalar ta hanyar bibiyar lambar da ke jikin fastar gayyatar taron.

Biyo-bayan wannan gagarumar nasara da jami'an suka yi yasa Gwamnan Jihar Malam Nasir el-Rufa'i ya bayar da umarnin rushe gidan da aka tsara yin baɗalar.

Gidan Sex Party Kaduna

Tuni dai tawagar rusau ta gwamnan ta cika aikinta yau 31 ga watan disambar shekarar 2020.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba