Hukumar farin kaya (DSS) reshen jihar Kano ta saki mawakin nan da ta tsare kan wakar batanci ga addinin musulunci da ya fitar.

DSS ta bayyana cewa ta kame mawakin tare da killace shi a wurin da yake da tsattsauran tsaro don kada fusatattun al'umma su kaddamar masa, duba da yadda wakar tasa ta ta tada hayaki a fadin Jihar.

Jami'an DSS
image: Department of State Service source: UGC
Sai dai kamar yadda bayanai da rahotanni suka tabbatar, mawakin ya bayyana nadamarsa karara tare da neman gafarar dukkan al'ummar musulmi, malam musulunci da kuma Gwamnatin Jihar Kano.

Kazalika mawakin ya shaidawa jami'an na DSS cewa sam bai san wakar tasa ta sabawa musulunci ba.

Idan baku manta ba, Sakataren Hukumar tace fina-finai, Isma'ila Afakallah ne ya mika rahoton mawakin ga hukumar ta DSS bayan ya samu daruruwan sakonnin korafi daga jama'ar gari a kan wakar ta batanci ga Annabi.

Jam'ian sun yi nasarar kama mawakin a wani otel da ya kwashe tsawon lokaci yana boye bayan ya saki wakar.

Da manema labarai suka tuntubi Malam Afakallah game da mawakin, Afakallah ya bayyana cewa yanzu haka matashin an sake shi ya koma cikin ahalinsa bayan shafe kwanaki masu yawa a tsare,
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba