Da safiyar yau 31 ga watan disambar 2020 ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya rattaɓa hannu akan kasafin kudin 2021.

Facebook/Muhammadu Buhari

Kamar yadda Malam Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na tiwita, Shugaban ya saka hannu ne akan kasafin kuɗin na shekara mai kamawa wanda adadinsa yakai Naira 13,588,027,886,175.

Kada dai a manta: Shugaban ya rattaɓa hannun ne mako guda bayan majalisar dokokin tarayya ta mayar masa da shi.

<
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba