Wata mata a dandalin sada zumunta na Facebook ta tona asirin wani malam dogo mabaraci da ya mallaki motoci biyar da  adaidaita sahu fiye da ɗaya.

Matar ta tabbatar da cewa mabaracin shine mafi arziki a cikin mabaratan jihar ta Enugu, a kudu maso gabashin Najeriya.

Matar mai suna Anastasia Micheal ita ce ta wallafa hotunan malam dogon, tace sananne ne shi a Shoprite ɗin Enugu, inda yake bara kullum.

Ƙwaƙƙwarar majiya ta bayyana cewa mabaracin ya mallaki motoci ƙirar minibus guda biyar da kuma keke napep da ba'a san adadinsu ba.

Motoci na napep ɗin nasa ya bayar da su ana masa haya da su.

Ta kuma bayyana mamakinka ƙarara kan yadda mabaracin ya ƙi dena bara duk da dukiyar da yake da ita, domin mutane dama sun san da dukiyar tasa.

Kalli hotunan mabaracin da kuma motocinsa harma da keke napep ɗinsa:

Mabaraci Mai Motoci

Mabaraci Mai Motoci

Mabaraci Mai Motoci

Mabaraci Mai Motoci

Anastasia ta wallafa, "Mabaraci mafi arziki a Enugu!"

"Wannan mutumin sanannen mabaraci ne a Shoprite ɗin Enugu, mutane da dama sun sanshi ne a matsayin mabaraci, amma a zahirance yafi waɗanda ke bashi sadakar arziki."

"Daga tabbataccen rahoto, yana da motocin haya guda biyar da kuma keke napep waɗanda yake kasuwanci da su."

"Dalilin da yasa ya ƙi daina bara bayan ya mallaki wannan dukiya shine abinda mutane da dama basu sani ba."

"Me kuke tunani?."

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba